Kotun Koli ta Najeriya ta sanya ranar Juma’a 17 ga watan Janairu a matsayin ranar da za a yanke hukunci kan shari’ar zaben gwamnonin jihohin Bauchi.
Alkalan kotun sun dage ranar hukuncin ne bayan da lauyoyin dake wakiltar bangarorin dake shari’ar suka tafka muhawara a kan bukatunsu.
Gabanin wannan mataki dai alkalan sun sanya ranar Litinin mai zuwa a matsayin ranar yanke hukunci kan shari’ar zaben Kano.
Sannan alkalan sun ce nan gaba za a bayanna ranar da za a yanke hukunci kan sauran kararraki 13 da ke gabansu kuma suke da dangantaka da zabe, ko kuma takaddama kan wani batu dake da nasaba da zaben.