Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2022 a ranar Juma’a, kamar yadda fadar shugaban kasa ta tabbatar.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Garba Shehu, ne ya tabbatar da hakan ga gidan talabijin na Channels a ranar Talata a Abuja.
A cewarsa, majalisar ta mika kasafin kudin shekarar 2022 kuma shugaban kasar zai rattaba hannu kan dokar da karfe 10 na safe.
Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan da ‘yan majalisar wakilai a zauren majalisar wakilai da na majalisar dattawa suka zartar da kasafin kudi na Naira tiriliyan 17.126, wanda ya kara farashin danyen mai daga dala 57 zuwa dala 62 kan kowacce ganga.
Cikakken bayani zai zo