Gwamnatin Kaduna ta tsawaita dokar hana fita har na tsawon wata daya a yunkurinta na dakile yaduwar cutar korona a jihar.
Gwamnatin jihar ta sanar da hakan ne a shafinta na Twitter cewa gwanma Nasir Elrufa’I ne ya tsawaita dokar bisa shawarwarin da kwamitin jihar kan cutar korona ya bayar karkashin jagorancin Mataimakiyar gwamnan jihar, Dr Hadiza Balarabe.
Gwamnatin Kaduna kuma ta ce za ta tilasta amfani da abin rufe fuska saboda muhimmancinsa wajen rage yaduwar cutar tsakanin mutane da kuma kare lafiyar jama’a.
A ranar 26 ga watan Maris ne gwamnatin Kaduna ta fara sanar da dokar hana fita a jihar, kuma yanzu Sanarwar ta ce dokar za ta fara aiki ranar Lahadi 26 ga Afrilu.
Gwamnatin ta umurci al’umma su zauna a gidajensu sannan wuraren ibada da shaguna da wuraren bukukuwa da kasuwanni za su kasance a rufe.
Har wala yau gwamnatin ta Kaduna ta ce za ta hukunta duk wanda ya saba wannan dokar ta hanyar tara da kwace motarsa.
Sannan gwamnatin Kaduna ta ce yadda cutar ke bazuwa, za ta rufe kofofin shiga jihar, kuma duk wanda aka kama ya shiga ko ya ratsa za a bukaci ya koma inda ya fito ko kuma a killace shi na tsawon mako biyu. Sannan gwamnatin ta ware ranar Laraba kawai a matsayin ranar bai wa al’umma dama su fita su yi siyayya su dawo gida su zauna.
Sannan za a zaftare albashin ma’aikatan jihar da kashi 25, yayin da Kwamishinoni da kuma Sakatarorin ma’aikatun gwamnatin aka nemi da kowannensu ya ba da tallafin Naira dubu dari biyar.