Abba

Ranar Litinin Abba Gida-Gida Zai San Makomarsa

Kotun Koli a Najeriya da ke sauraron kararrakin zaben gwamnonin wasu jihohi ta dage zaman hukuncin zaben jihar Kano.

Kotun ta ce sai ranar Litinin 20 ga watan Janairun 2020 za ta yanke hukunci kan shari’ar da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP yake kalubalantar Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC da kuma hukumar INEC.

Lauyoyin bangarorin sun shafe sama da sa’a daya suna tafka muhawara kafin alkalan su yanke hukuncin dage zaman.

Kazalika, rukunin alkalan sun kuma saurari kararrakin zaben jihohin Bauchi da Sokoto da Imo da Benue da kumaFilato.

Tun a jiya Litinin ne kotun ta fara zama kan shari’o’in amma sai aka dage zaman zuwa yau Talata sakamakon abin da ta kira “rashin lafiyar” daya daga alkalai bakwai da za su yanke hukunce-hukuncen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *