By Ishaq Dabai
Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya yi afuwa ga fursunoni 18 da aka daure a gidajen kurkukun dake jihar.sannan Akeredolu ya kuma daure wasu fursunoni 26 da aka yan kewa hukuncin kisa.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai, Richard Olatunde, ya sanya wa hannu, Olatunde ya ce wannan karimcin da gwamnan yayi shine don tunawa da ranar samun ‘yancin kai na wannan shekarar.
Sanarwar tace “A cikin yin amfani da ikon na sakin layi (d) na ƙaramin sashe na (1) na sashe na 212 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya,na shekarar 1999 kamar yadda aka gyara, Gwamnan Jihar Ondo, Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu, SAN, yayiwa Fursunoni 18 a fuwa wadanda aka yanke wa hukuncin zaman gidan kaso.
“Gwamnan ya kuma daure wasu fursunoni ashirin da shida 26 wadanda kotuna daban daban na jihar suka yanke wa hukuncin kisa.
An saki wadanda aka yankewa hukuncin ne bayan sun nuna nadama da kuma halaye masu kyau a cibiyoyin gidan gyaran hali ”Yayin daya umarce su dasu kasance masu kyawawan halaye da yin rayuwa ba tare da aikata laifi ba ana gaba, gwamnan ya bukaci jama’a da kada su nuna musu wariya yayin da suke sake komawa gida cikin al’umma.