Rundunar Sojin Kasarnan ta bukaci al’umma da ka da su firgita da jin tashin harbe-harben manyan bindigogi a ranar bikin samun ‘yancin kan kasar nan da ke tafe.
Rundunar Sojin ta fadi hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun mataimakin daraktan hulda da fararen hula na rundunar, Kaftin Haruna Tagwai, a ranar Asabar, a Abuja.
Tagwai ya ce, an shirya gudanar da faretin bikin samun ‘yancin kan na 59 ne a ranar 1 ga watan Oktoba, a farfajiyar fadar Shugaban kasa da ke Abuja.
Ya tabbatar da cewa cikin bukukuwan da aka shirya akwai bikin al’ada na harba manyan bindigogin atilari a lokacin bikin.
Ya ce; a don haka ne suke sanar da al’umma musamman wadanda suke da zama a Asokoro, Maitama da sassan ta da ke kusa, kar su razana a lokacin da suka ji tashin harba manyan bindigogin a lokacin bukin.