Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce bikin rantsar da Dr William Ruto a matsayin shugaban kasar Kenya na 5 bikin dimokuradiyya da cibiyoyin dimokuradiyya a Afirka ne.
Farfesa Osinbajo ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan bikin rantsar da Ruto da aka gudanar a filin wasa na Moi International Stadium da ke Nairobi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Osinbajo Ya Ketare Zuwa Kenya Domin Wakitar Buhari
Mataimakin shugaban kasar, yayin da yake magana kan muhimmancin bikin rantsar da shugaba Ruto, ya ce, “Biki ne na dimokuradiyya, kuma dalilai a bayyane suke, hukumomin da aka kafa – IEBC (Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta) da ta yi daidai da namu INEC. da bangaren shari’a; sun ci gaba da tabbatar da cewa ba wai kawai an bi matakai yadda ya kamata ba har ma an yi adalci.
“A duk lokacin da muka yi magana game da bikin dimokuradiyya, hakika muna magana ne game da bikin cibiyoyinmu, cibiyoyin da suka durkusar da dimokradiyya da bin doka da oda.”
“Ina tsammanin abin da muka gani a nan Kenya da kuma rantsar da Dr Ruto hakika shaida ce ta cibiyoyi masu karfi na yin abin da ya kamata su yi.”
“Wannan babban misali ne kuma dukkanmu mun gamsu sosai. Kuma na tabbata kun ga daga dukkan shugabannin kasashen Afirka da wakilansu da suke nan a yau, cewa akwai yanayi na jin dadi domin hakan ya yi tasiri.”
Babban abin da ya fi daukar hankali shi ne bikin rantsar da sabon zababben shugaban kasar da mataimakinsa – Rigathi Gachagua, da kuma mika kayan mulki da kwafin kundin tsarin mulkin Kenya daga tsohon shugaban kasar Uhuru Kenyatta ga Dr Ruto.
Bikin ya samu halartar shuwagabannin kasashen Afrika 20 da wakilansu, da suka hada da shugabanin Afirka ta Kudu – Cyril Ramaphosa, Chadi – Mahamat Idriss Deby, Tanzaniya – Samia Suluhu, Seychelles – Wavel Ramkalawan, Uganda – Yoweri Museveni, Rwanda – Paul Kagame, Sudan ta Kudu – Salva Kiir, Burundi – Évariste Ndayishimiye, Zimbabwe – Emmerson Mnangagwa, da Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, da sauransu.
Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce tun da farko da suka isa filin jirgin Jomo Kenyatta na Nairobi, Farfesa Osinbajo ya samu tarba daga tsohon gwamnan yankin Kwale, Hon. Salim Mvurya, da babban jakadan Najeriya a Kenya, Amb. Yusuf Yunusa, da sauran jami’an hukumar.
A wani labarin kuma, An Rantsar Da Sabon Shugaban Ƙasar Kenya, Bayan Nasara A Zaben Kasar
Sabon shugaban kasar Kenya, Mr Willaim Samoei Ruto ya dauki rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Kenya na Biyar.
Babban magatakardan ma’aikatar shari’a ne ya rantsar da sabon shugaban, yayin da taron daka gudanar yau, wanda ya samu halartar dubban mutane daga cikin da wajen kasar.