Kamar yadda aka gudanar a sauran jihohin Nigeria ciki har ma da babban birnin Tarayya Abuja, jihar Yobe ita ma ta bi sahu wajen zaɓen shuwagabanin Jam’iyar APC na matakin jiha.
Da yake jawabi a taron, Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, yace rarrabuwar kawuna tsakanin ƴan jam’iya ɗaya babbar matsala ne wanda yake haifar da koma baya.
Yace muddin ba a guji halin rabuwar kai ba, tofa ba za’a rabu da matsaloli ba a jam’iya, yana mai yaba da yadda Mambobin Jam’iyar APC na jihar Yobe, suka bada goyon baya da haɗin kai wajen zaɓen shuwagabanin Jam’iyar a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna El’-Rufa’i Dan Dimokuradiyya ne na zahiri, inji Sanata Uba Sani
Ya kuma ja hankulan jama’a da su kasance masu addu’a da kyakkyawan fata ga shuwagabanni a ko da yaushe.
Shima a nashi Jawabi, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan bayyana shugabancin Mai Mala Buni daga matsayin Gwamna har zuwa Jam’iyar APC a matakin Tarayya, a matsayin gyara ga Nigeria baki ɗaya, bisa la’akari da yadda ya sulhunta ƴan Jam’iyar, wanda hakan ya jawo wasu ƴan siyasa zuwa cikin Jam’iyar ta APC.
Sanata Ahmed Lawan ya yi kira ga ƴan jihar Yobe da su ƙara goyon bayan Gwamnatin Buhari domin ta samar musu da duk abun da suka buƙata a ƙarƙashin mulkin Dimokuraɗiyya.
Shima da yake jawabi, Shugaban Kwamitin zaɓen shuwagabannin Jami’iyyar APC na jihar Yobe sanata Osita Izunaso, yace wannan zaɓe yin sa yana daga cikin sharuɗɗan da aka shimfiɗawa Jam’iyar APC a kai.
Ya kuma janyo hankulan sabbin shuwagabanin da aka zaɓa da su dage wajen sauke nauyi da ya rataya a wuyan su.
Alhaji Muhammad Gadaka shine aka zaba a matsayin shugaban Jam’iyar a matakin jiha, a yayin da kuwa aka zabi Alhaji Abubakar S. Bakabe a matsayin Sakatare.
Jaridar Dimokuradiya ta ruwaito cewa an yi zaben bisa yerjejeniya wato- onsensus a turance, kuma anyi zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana.