A Kasar Rasha hukumomi na tsare da fitaccen dan jaridar nan, Ivan Golounov wanda ya shahara a kan aikin jarida na binciken ko-kop.
Ana dai zargin dan jaridar ne da safara hodar cocaine mai yawan gaske a cikin jakar da yake dauke da ita a baya. ‘Yan sanda sun ce sun kamashi dauke da hodar ta cocaine kilo hudu. Ivan Golounov wanda ke aiki a jaridar Meduza mai zaman kanta a Rasha ya cika sukar gwamnatin a rubuce- rubuce da yake yi.