Ma’aikatar Lafiya ta Rasha ta bayyana cewa ƙasar ta fara haɗa sabon riga-kafin cutar korona da ta ƙirƙiro.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da ta fitar, inda ma’aikatar ta bayyana cewa za a samar da wannan riga-kafin zuwa ƙarshen watan Agusta domin amfanin mutane baki daya.
A bangare guda kuma, masana na ganin cewa wannan yunƙurin da Rasha ke yi na gaggawar fitar da wannan riga-kafin kan iya kawo cikas ga lafiyar bil’adama, lamarin da wasu kuma ke ganin abin ba haka yake ba.