A jiya Litinin Rasha ta yi barazanar katse bututun Man ta da ke zuwa Jamus, Mundun kasashen yamma suka dauki matakin kakabawa kasar takunkumi kan fitar da Man fetur.
Mataimakin Firayim Minista, Alexander Novak, ya ce irin wannan matakin zai haifar da “mummunan bala’i” ga Tattalin arzikin duniya da kuma haifar da farashin mai ya rubanya zuwa dala 300.
Haryanzu dai Kasar Amurika na ci gaban da tuntubar kawayanta domin lalubo hanyar da zata ladaftar da Rasha bisa mamayar da takeyi a Ukraine. Amma kasar Jamus da Netherland sun yi fatali da Kudirin.
Kazalika Wani kididdiga ya nuna cewa, Kasashen Turai na samun kashi 40 na Iskar Gas din su ne, da kuma Kashi 30 na Mai daga kasar Rasha, Kuma yana da matukar wuya su iya samar da wata hanyar, idan Rasha ta dauki wannan Mataki.
A wani labarin na daban
Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, a ranar Talata ya jaddada cewa har yanzu shi ne gwamnan jihar ba tare da la’akari da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke ba.
Kotu ta kori shi (Umahi) da mataimakinsa, Dakta Kelechi Igwe daga ofishin su tare da umurtar mutanen biyu kada su ci gaba da bayyana kansu a matsayin masu rike da mukami.
Da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke sabon gidan gwamnati, Abakaliki, Gwamna Umahi wanda ya bayyana hukuncin a matsayin “adalcin daji da aka saya” ya bayyana cewa hukuncin ba wani ci gaba bane ga bangaren shari’a.
Idan dai za’a iya tunawa a yau ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi da mataimakin sa Eric Kelechi Igwe da su gaggauta ficewa daga ofishinsu bayan sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC ba bisa ka’ida ba.
Mai shari’a Inyang Ekwo, a wani hukunci da ya yanke a ranar Talata, ya bayyana cewa bayan ficewa daga jam’iyyar a wanne dandalin da suka lashe zaben, Umahi da Igwe ana ganin sun yi murabus daga ofishinsu.
Mai shari’a Ekwo ya umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta karbi sunayen mambobinta daga hannun jam’iyyar PDP domin maye gurbin Umahi da Igwe, domin cika ragowar wa’adin mulkinsu, ko kuma ta sake gudanar da sabon zabe domin maye gurbin Umahi da Igwe.
An yanke hukuncin ne kan karar da PDP ta shigar, inda INEC, APC, Umahi da Igwe a matsayin wadanda ake kara.