Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya bayyana cewa cin hanci da rashawa yana daya daga cikin manyan abin da ke sanya miliyoyin ‘yan Nijeriya ke shan wuya a kasarnan.
Buhari ya kara da cewa; rashawa a kowanne mataki shi ne babban kalubalen da yake durkusar da tattalin arzikin Nijeriya tare da kawo cikas ga ci gaban kasar. Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi a taron shekara-shekara kan tattalin kudi da Makarantar koyar da tattalin kudi wato ICAN ta gudanar a Abuja.
Shugaban kasar wanda Sakataren gwamnati, Boss Mustapha ya wakilce shi, ya tabbatar da cewa yakin da suke yi domin kawo karshen rashawa a Nijeriya, na gaske ne, kuma nasarar wannan yakin ne kawai zai kawo ci gaba a gaba. Ya kara da rashawa rashawa kamar take hakki ne.
Sannan ya kara da cewa; rashawa yana durkusar da tattalin arziki, da rashin shugabanci nagari, da watanda da kudin al’umma da kuma durkusar da hannayen jari. Ya ce dole ne gwamnatinsu ta yaki rashawa.