Gwamnan Jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya amince da sauke Injiniya Mu’azu Magaji Ɗan sarauniya, daga muƙamin sa na shuagaban Kwamitin Man Fetur da aikin samar da bututun Iskar Gas na Jahar, nan take saboda rashin ƙwazo wajen gudanar da ayyukan sa.
Korar shugaban ya biyo bayan rashin ƙoƙarin shu wajen samar da ayyuka, da rashin ƙoƙarin da ya kamata da sauran wasu matsaloli.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ƴada Labaru Malam Muhammad Garba ya sanya wa hannu, inda ya bayyana cewar naɗa Magaji a watan Afrilu, domin ya jagoranci kwamitin tare da manufar zaiyi aiki yadda ya kamata domin tabbatar da gudanar da aikin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari ya ware biliyan 1.6 domin sayen motocin sa, amma Miliyan 650 kaɗai ya ware domin aikin wutar lantarkin Mambilla
Acewar sanarwar, abun mamaki ya gaza yin aikin da ya kamata yayi wanda aka ɗora mashi.
Sanarwar ta ƙara dacewa Shuwagabancin sa na kwamitin wanda zaiyi aiki ne domin tabbatar da haɗin gwuiwa da Kamfanin NNPC wajen tabbatar da aiwatar da aikin, amma hakan bai samu ba domin kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
Sanarwar ta ɓukaci korarren shugaban daya miƙa mulkin kwamitin ga mataimakin sa Aminu Babba Ɗan Agundi, Sarkin Dawaki Babba.
Gwamna Ganduje ya kuma gode masa daya yiwa jahar aiki, sai yayi mashi fatan nasara a rayuwar sa.
Comments 1