Gwamnatin Tarayya ta bukaci matasa da mata da su kara samun sana’o’i don samawa kansu ayyukan yi da inganta hanyoyin samar da kudaden shiga a kasar nan.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Babbar Sakatariya ta ma’aikatar kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire Monilola Udoh ce ta yi wannan kiran a yayin wani shirin horar da ma’aikata kan albarkatun halittu da aka shirya wa matasa da mata marasa aikin yi a garin Ibadan na jihar Oyo, in ji sanarwar da ma’aikatar ta fitar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Akwai Yiwuwar Kano Ta Fuskanci Wata Ambaliyar Ruwa – NiMET
Udoh ta ce shirin horar da ma’aikata wanda gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar jihar Oyo suka shirya, ya bayyana mahalarta taron kan fasahar kere-kere da sabbin hanyoyin amfani da albarkatun halittu domin inganta kudaden shiga da samun ingantacciyar rayuwa.
Ta ce horon yana kuma da nufin rage rashin aikin yi domin baiwa ‘yan Najeriya damar samun kudin shiga don dogaro da kai ta hanyar amfani da albarkatun halittu da kuma amfani da su.
Jaridar Daily Trust Ta ce halin da ake ciki na rashin aikin yi a kasar nan babbar barazana ce ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.
A wani labarin kuma: Akwai Yiwuwar Kano Ta Fuskanci Wata Ambaliyar Ruwa – NiMET
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargadin cewa bisa la’akari da yadda aka samu ruwan sama da kuma adadin ruwan sama da aka samu a cikin watan Agusta, Kano na iya fuskantar ambaliyar ruwa a watan Satumba.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewa hukumar ta yi wannan gargadin ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Muntari Ibrahim a ranar a wannan makon.
A wani labarin kuma: Gwamnan Neja Ya Bayar Da Umarnin Gaggauta Rushe Wasu Gine Gine
Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya umarci ma’aikatar muhalli da ta hada hannu da ma’aikatu da ma’aikatar karamar hukumar Kontagora domin ruguza duk wasu gine-gine.
Gwamna ya ce hakan zata faru ne akan duk wani gini da ya hau kan hanyoyin ruwa.