Hadaddiyar kungiyar kwadagon Nijeriya ta bayyana cewa a shirye take ta fantsama yajin aiki a kan rashin biyan karancin albashin naira dubu 30 da gwamnati ta yi, don haka ‘yan Nijeriya su zauna cikin shiri.
Rahotanni sun tabbatar da cewa; kwamitin kungiyar kwadago dake tattaunawa da gwamnatin tarayya game da tsare-tsaren aiwatar da fara biyan karancin albashin ne ta bayyana haka a ranar Talata, 17 ga watan Satumba, inda ta yi kira ga ‘yan Nijeriya su roki gwamnati ta yi abin da ya kamata kafin ta dauki mataki.
Shugaban kwamitin, Simon Anchaver da Sakatarensa Alade Lawal ne suka fitar da wannan sanarwa a babban birnin tarayya Abuja, inda suka ce sun baiwa gwamnati isashshen lokacin duba bukatun ma’aikata tare da biyan bukatain, amma alamu sun nuna gwamnati ba ta da burin cikawa. Don haka kwamitin ta ce ba za ta sake gargadin gwamnati game da wannan batu ba, sai dai kawai uwar kungiyar kwadago ta umurci ma’aikatan Nijeriya su fara yajin aiki irin na sai baba ta gani a kan wannan batu na rashin biyan karancin albashin Naira 30,000.