Daruruwan Likitoci da ma’aikatan lafiya a asibitocin gwamnati da na masu zaman kansu a Nijeriya suna gudun duba masu cutar Korona sakamakon rashin kayan aikin kariyar kai daga kamuwa da cutar.
Kayayyakin aikin sun hada da; abin hannu, gilashin ido, rigar kariya, abin rufe kai, takunkumin fuska, na’urar numfashi, takalmin kariya da sauran su.
Wadansu Likitocin da ma’aikatan lafiya da masu gwaje-gwaje a dakin gwajin cuta tuni suka koma cibiyoyin killace al’umma da suke dauke da cutar Korona, inda wasu kuma suka killace kawukansu a gida domin jiran sakamakon gwajin cutar na su.