Gwamnan Jahar Benue Samuel Ortom a ranar Laraba yayi kira ga Fulanin Nigeria, dasu yi magana akan shigowar da Fulani na Ƙasar waje keyi a wasu al’ummomin Nigeria.
Ortom yayi wannan kiran ne a lokacin da ya karɓi tawagar masu riƙe da Sarautun gargajiya daga Jahar Nasarawa , wanda a madadin gwamnatin Jahar suka kai ziyarar ta’aziyya ga Gwamnan Jahar Benue.
Tawagar ta samu jagorancin Mai Martaba Sarkin Keffi Dr Shehu Chindo, inda ya samu rakiyar wasu masu riƙe da Sarautun gargajiya daga Jahar Nasarawa domin yin ziyarar ta’aziyya, ga Gwamna Ortom da Majalisar Sarakunan Gargajiya na Jahar Benue, akan wata rasuwar Ochi’Doma Elias Ikoyi Obekpa na Idoma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari ya yabawa Erdogan akan tausayin sa ga ƴan gudun hijira
A cewar Gwamnan ” Al’ummar Yaren Tiv da Fulani da Sauran ƴan Najeriya suna zaune cikin zaman lafiya, kafin Fulanin ƙasashen waje da aka ƙyale suka shigo ƙasar, suka haddasa ta’addancin dake faruwa a yanzu.
“Zaifi kyautuwa idan Fulani suka yi magana akan shigowar wasu Fulani daga ƙasashen waje.”
Gwamna Ortom yace dokar hana kiwo a fili ta Jahar bata da nufin ɓatawa wani, amma abune dai-dai ga Makiyaya da Manoma.
Shugaban tawagar kuma Sarkin Keffi Dr Shehu Chindo ya gabatar da takardar jaje ga Gwamna Ortom daga Gwamnan Jahar Nasarawa, yace labarin mutuwar Ochi’Doma abun baƙin ciki ne ga Jahar Benue, Nasarawa da Ƙasa baki ɗaya.