Daga Usman Salisu Gurbin Mikiya
Shugaban Cocin Redeemed Christian of God, Fasto Enoch Adebayo a ranar Asabar din nan yayi Allah wadai, akan harin da Yan ta’adda suka kaima wani Sarki a Jahar Ekiti, inda ya bayyana haka a matsayin tsantsar rashin Martaba Sarakunan Gargajiya.
Adebayo wanda ya tabbatar dacewa Allah Madaukakin Sarki zai kawo Karshen Dukkanin ta’addan ci a Najeriya, ya bukaci yan Najeriya dasu cigaba da yiwa Kasar nan addu’o’i domin cigaban ta, ta la’akari da matsalolin dake fuskantar ta.
Faston yayi wanna jawabin ne a Ado Ekiti Babban Birnin Jahar, a lokacin daya kaiwa Gwamnan Jahar Kayode Fayemi ziyara.
Yace masu rike da Sarautun Gargajiya sun cancanci a rika girmama su, ta la’akari da Mahimmiyar rawar da suka takawa a cikin Al’umma.
Idan dai ba’a manta ba JARIDAR DIMOKRADIYYA ta kawo maku rahoton cewa, yan ta’adda sun kaiwa Sarakuna biyu hari na Jahar, da suka hada da Elewu na Ewu Ekiti Oba Adetutu Ajayi, wanda ya tsallake rijiya da baya, da akayi nufin sace shi, da kuma Obadu na Ilemeso Ekiti Oba David Oyewumi wanda aka sace a fadar sa a ranar Alhamis, wanda har yanzu ba’a san inda yake ba