A jawabin da ya yi wa manema labarai bayan wata tattaunawa ta tsaro tare da Buhari, mai ba da shawara kan tsaro, Janar Babagana Monguno (mai ritaya), ya ce shugaban kasar ya kalubalanci hafsoshin tsaron kasar da su sake kokarinsu.
A cewar Monguno, Shugaban ya ce, duk da cewa shugabannin tsaron sun yi iya kokarinsu, amma abin da suka yi bai dace da kalubalen da kasar ke fuskanta ba a halin yanzu.
Ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan rashin jituwar da ke tsakanin jami’an tsaro tare da daukar nauyin bangarorin tsaro daban daban da su yi aiki tare don magance matsalolin tsaron kasar.
Saboda haka ya ba da sanarwar cewa ba za a kara yarda da uzurin kowa ba, kamar yadda ya ce yana bada umurni ga jami’an tsaron kowanne dan kasa ya yi rayuwa mai dadi a Kasar.