IG Adamu

Rashin Tsaro A Kasashen Yarabawa: An Tsaurara Tsaro A Yankin

Sufeton Janar na ‘yan Sandan Nijeriya, Muhammed Adamu a ranar Talata ya bayyana cewa; za a aike da tawaga ta musamman masu kwarewa ta musamman  domin gudanar da atisaye a yankin kudu maso yammacin Nijeriya domin magance matsalolin tsaro dake fuskantar yankin.

A yayin da yake yiwa jami’an ‘yan sanda jawabi a wata ziyara da ya kai ofishin ‘yan sanda dake jihar Osun reshen Osogbo, Sufeto Adamu ya ce wannan matakin da za a dauka wani mataki ne da zai kawo karshen rashin tsaro a yankin.

Sannan ya ce daya daga cikin manufar ziyararsa shi ne domin ya yi jami’an bayani akan matakan da aka fitar a taron tsaro da ya gudana a garin Ibadan na jihar Oyo a ranar Litinin. Sannan ya tabbatar da cewa; ya kuma zo ne domin karfafa jami’an domin ganin sun dakile ayyukan bata gari da hare-hare da sace-sacen ‘yan bindiga a jihar da ma yankin baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *