By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Alhamis ne mai baiwa gwamna Aminu Masari shawara kan harkokin tsaro, Malam Ahmad Katsina, ya tabbatar da cewa an dage dakatar da harkokin sadarwa a wasu kananan hukumomin jihar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an rufe hanyoyin sadarwa a cikin watan Satumban daya gabata a kananan hukumomin sha uku da suka hada da Sabuwa, Faskari, Dandume, Batsari, Danmusa, Kankara, Jibia, Safana, Dutsin-Ma, Funtua, Bakori, Malumfashi da Kurfi, a wani mataki na magance matsalolin tsaro da ake fuskanta a yankunan jihar.
Gwamnatin jihar ta kuma bayyana wasu matakan tsaro da suka hada da rufe hanyar Kankara-Sheme da kuma hanyar Jibia-Gurbin-Baure ga masu ababen hawa, dakatar da sayar da dabbobi a kasuwanni a kananan hukumomi goma sha hudu da kuma hana sayar da man fetur da bai wuce Naira 5,000 ga kowane direba a tashoshin gidajen mai biyu a cikin majalissu goma sha hudu ba.
Haka kuma gwamnati ta takaita zirga-zirgar masu tuka babura da masu tuka keke daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safe a babban birnin jihar Katsina da kuma daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe a duk yan kunana kananan hukumomin da tsarin sadarwa ya shafa.
Sauran matakan da Gwamnati ta bayyana sun hada da hana siyar da babura a kasuwar Charanchi da safarar shanu tsakanin jahohin kasar da kuma hana manyan motoci daukar itace daga daji.
Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Muhammed Inuwa ne ya bayyana haka a wata zantawa da manema labarai na baya-bayan nan, inda ya ce matakan tsaro sun kawo raguwar ayyukan ta’addanci a jihar musamman ‘yan fashi da garkuwa da mutane, duk da cewa mazauna yankin sun yi zargin cewa rufe hanyoyin sadarwa ya hana wadanda harin ‘yan bindiga ya rutsa da su nema taimakon gaggawa daga jami’an tsaro lokacin da aka kai musu hari.