Masu garkuwa da mutane sunyi awan gaba da mutane da dama wadanda ba san adadinsu ba, a lokacin da suka tare hanyar Sokoto zuwa Gusau. Jaridar Tvcnews ta wallafa a shafinta
Da dai yammacin ranar Lahadi ne, Yan bindigan suka rufe hanyar Sokoto zuwa Gusau daidai kauyen Dogon Karfe, inda suka fara harbin mai kan uwa da wabi, wanda hakan ya sanya dole masu Motoci tsayawa.
Kamar yadda Jaridar Tvcnews ta ruwaito, tace mafiya yawan Fasinjojin da aka kwashe suna cikin Motoci uku ne, wadanda motocun mallakin gwamnatin Jahar Sokoto ne.
KARANTA:- Kawo karshen matsalar tsaro: Gwamna Masari ya ba gwamnoni shawara
A satin da ya gabata ne ranar Laraba, yan bindigan suka tare hanyar Sokoto zuwa Gusau a dai dai-dai gurin da sukayi na ranar Lahadi, inda suka tafi da matafiya goma sha biyu, sai daga bisani jami’an tsaro suka kubutar dasu.
Kawo yanzu dai, jami’an Yan sanda na Jahar Zamfara basu bada sanarwar aukuwar lamarin ba, duk da anyi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun jami’an Yan sandan na Jahar Zamfara amman abun yaci tura.
A wani labarin, Masari yayi kira a tallafawa matasa, hakan zai kawo saukin rashin tsaro
Gwamnan Jahar Katsina Aminu Bello Masari ya janyo hankalin shuwagabanni kan wadata matasa da ayyukan yi, hakan na daga cikin hanyoyi da zai rage matsalar tsaro dake addabar kasar nan.
Gwamna Aminu Bello Masari yayi wannan kira ne ta hannun Alhaji Ibrahim Musa Kalla, babban Sakataren mataimakin gwamnan Jahar Katsina., .
Gwamnan yace, baiwa matasa hanyoyi daban-daban zai hanasu fadawa cikin muggan ayyuka.
Kamar yadda yace, ” Wajibin mune mu ciyar da yankinmu gaba, muna da bukatar masu hannu da shuni sun fara tallafawa matasa dake yankunan mu.”
Wajibin Kungiyoyi masu zaman kansu, da daidaikun mutane da wasu Hukumomi su cigaba da sanya hannu a cikin wannan lamarin.
Gwamna Masari yace ingantacce ilimi gami da taimakawa matasa shine kawai zai hana matasa fadawa cikin muggan ayyuka.
“Idan muka ilimantar da matasa zamu rage yawan masu garkuwa da mutane, mu fara daukan dawainiyar karatun wasu dake yankinmu domin tallafawa garuruwan mu.