Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya bayar da umurnin hana amfani da babura a yankunan Mbamba, Yolde Pate da Ngurore na karamar hukumar Yola ta Kudu.
Ya kuma haramta amfani da su a Viniklang da Federal Housing Estate a karamar hukumar Girei daga karfe 5 na yamma zuwa 5 na safe.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Humwashi Wonosikou ya fitar a ranar Talata.
Sanarwar ta ce, “Hukumar hana zirga-zirgar babura ta jihar Adamawa mai lamba 1 ta shekarar 2022 ta fara aiki ne a ranar Talata, 8 ga Fabrairu, 2022 har zuwa fitar da wata sanarwar.”
Gwamnatin jihar ta ce ta sanya dokar ne domin dakile karuwar ayyukan masu aikata laifuka da ke kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.
“Sun zama barazana ga zaman lafiya, walwala, tsaro da kwanciyar hankali na tsarin siyasa da tattalin arzikin jihar, da kuma tasirinsu ga ci gaba wanda ya zama dole ne a dakile su yadda ya kamata,” in ji shi.
Dangane da odar, duk mutumin da aka samu akan babur ya na tafiya, a cikin lokacin da aka haramta ko a matsayin mahaya ko fasinja zai fuskanci hukunci.
Duk da hakaa gwamnatin ta keɓe waɗanda ke da dalilai na gaske kamar neman kulawar likita, ba da kulawa da taimako ga masu rauni ko balaguro don aikin da aka keɓe na musamman Kuma mai mahimmanci.