By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo ya bayar da umarnin rufe gidajen shakatawa na Mai Asubahi da Gidan Barau dake garin Ore a karamar hukumar Odigbo a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mista Richard Olatunde, babban sakataren yada labaran sa ya fitar ranar Talata a Akure.
Akeredolu ya bayyana cewa wannan umarnin ya biyo bayan karuwar matsalolin tsaro da mazauna garin Ore suke fuskanta.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Olatunde yace an bayar da umarnin rufe wuraren ne biyo bayan aikata laifuka da wasu gungun ‘yan bindiga da aka fi sani da “Zamfara Boys’ wadanda suka kware wajen safarar miyagun kwayoyi da kuma yin lalata da kananan yara.
Saboda haka gwamnan ya umarci kwamandan hukumar tsaro ta jihar, (Amotekun) daya tara jami’ai domin aiwatar da wannan umarni, in ji Olatunde.