By Ishaq Dabai
Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce ta dauki kwararan matakai na hana ‘yan fashin dake tserewa a halin yanzu dan gane da jerin hare haren sojoji a Arewa maso Yamma, daga shiga jihar.
Gwamna Abdullahi Sule, ya fadi haka ne lokacin tattaunawa kan batun tsaron jihar da aka gudanar a gidan gwamnati, a Lafiya babban birnin jihar a ranar Talata.
Sule, wanda ya bayyana fargabar cewa ‘yan fashin da ke tserewa a halin yanz, na iya neman mafaka a galibin sassan jihar da ba za a iya shiga ba, irin na haramtacciyar kungiyar Darussalam, ya ce ya zama wajibi ga mambobin kwamitin tsaro, dasu tattauna yanayin tsaro a duk fadin kasar kamar yadda yake shafar Jihar Nasarawa.
Gwamnan, ya ce akwai bukatar jihar ta dauki kwararan matakai, ta yadda za a iya kauce wa yiwuwar ka sancewar wadannan ‘yan fashin da ke tserewa daga mafakar da suke a jihar Nasarawa, da kuma kare mutanen jihar.
Ya kuma taya Shugaba Muhammadu Buhari, da hukumomin tsaro, murnar nasarorin da ake samu a yaki da ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane a fadin kasar nan.
Ya nuna damuwar sa kan cewa nasarorin da aka samu a halin yanzu akan ‘yan bindiga a Neja, Zamfara, Kaduna da sauran jihohin Arewa maso Yamma, na iya zama barazana ga zaman lafiya a jihar Nasarawa.
Ya yabawa hukumomin tsaro da ke aiki a kananan hukumomi 13 na jihar, musamman ‘yan sanda, DSS da jami’an tsaro na farin kaya , saboda rawar da suka taka kwanan nan, wajen kama masu garkuwa da mutane da ke aiki a kan hanyar Akwanga zuwa Jos, wanda ya kai ga kubutar da wasu, wadanda abin ya shafa.