A ranar Asabar din da ta gabata ne gwamnatin jihar Katsina ta sanar da bude duk gidajen mai da kasuwannin shanu da aka rufe saboda satar shanu da kuma ‘yan fashi daji a jihar.
Sakataren gwamnatin jihar Muhammad Inuwa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da kakakin sa Abdullahi Aliyu -Yar’adua ya fitar.
Sanarwar ta ce Gwamna Aminu Masari ya amince da wannan umarni.
Ya kuma bayyana cewa Masari ya umurci Masarautun biyu na jihar Katsina da Daura da su gargadi hakimai da sarakunan kauyukan yankunan da abin ya shafa da su yi taka-tsan-tsan tare da tabbatar da cewa “ba a yarda da duk wani aiki na hadin gwiwa na Sarakunan Fawa da wasu su ba.”
Sanarwar ta yi gargadin cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen sake sanya dokar rufe kasuwannin inda aka lura da sake bullar wani shakku game da lamarin.
A watan Satumbar 2021 ne jihar Katsina ta sanar da rufe wasu kasuwanni a wani bangare na dabarun magance matsalar rashin tsaro a jihar.
Sauran matakan sun hada da rufe hanyar Jibia zuwa Gurbin da Baure da kuma hanyar Kankara zuwa Sheme da Motocin Yan kasuwa ke bi.