Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa na neman a kafa ‘yan sandan jihohi domin tunkarar kalubalen tsaro a yankin da ma kasa baki daya.
Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya ce taron da aka gudanar a Abuja a daren ranar Litinin din nan ya duba matsalar tsaro a yankin Arewa da sauran al’amuran da suka shafi ci gabanta tare da kuduri aniyar tallafa wa gyaran kundin tsarin mulkin kasar domin ya dace da kafa ‘yan sandan jihohi.
A cewar sanarwar, a ranar Talata, ta bakin Daraktan yada labarai da hulda da jama’a, Dr. Makut Simon Macham, gwamnan ya ce matakin zai magance kalubalen tsaro yadda ya kamata da kuma yadda ake bukata a yankin.
Karanta kuma: Shugabannin Majalisun Najeriya Sun Amince Da Kafa ‘Yan Sandan Jihohi
Kungiyar gwamnonin Arewa ta sake nanata kudurinta na bunkasa makamashin hasken rana saboda kwatankwacin fa’idar yawan hasken rana a yankin.
A saboda haka ne aka amince baki daya cewa za a girbe megawat 2,000 na wutar lantarki a fadin jihohin kasar nan 19 da Abuja da zummar yin amfani da dimbin karfin hasken rana.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Taron dai ya yi nadamar yajin aikin ASUU ( kungiyar malaman Jami’o’i ) da ta yi imanin cewa ya fi daukar hankali a yankin, saboda yawancin daliban yankin suna halartar makarantun gwamnati.
Don haka kungiyar ta roki malaman jami’o’in da su “ba gwamnatin tarayya hadin kai wajen sasanta rikicin”.
A wajen taron akwai gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya; Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari; Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu; Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum; Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello; Gwamnan jihar Taraba, Darius Dickson Ishaku; da mataimakan gwamnonin jihohin Adamawa, Benue, Nasarawa da Jigawa.
Jaridar SOLACEBASE ta rawaito Sarakunan gargajiya da suka halarci taron sun hada da Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III; Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi; Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero; Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli; Sarkin Fika, Alhaji Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa; Sarkin Lafia, Mai shari’a Sidi Bage Muhammad; Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad, Sarkin Gumi, Mai shari’a Lawal Hassan Gumi; Attah Igala, Mathew Opaluwa; Ochi’Idoma, Fasto John Elaigwu; da Aku Uka na Wukari, da Dattijo Manu Ishaku Adda Ali, da sauransu.
A wani labarin kuma: Gwamnatin Kano Ta Musanta Siyar Da Harabar Wasu Kotunan Jihar
Shugaban kwamitin tattaunawa da gyaran wasu wurare mallakar gwamnatin jihar Kano, Barista Musa Abdullahi Lawan, ya bayyana ikirarin cewa gwamnatin Kano ta sayar da wasu kotunan shari’a ga wasu mutane da cewa labarin ƙanzon kurege ne.
Shugaban wanda kuma shi ne Babban Lauyan gwamnatin Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a ya mayar da martani ne kan ikirarin da wasu Lauyoyin Jihar Kano, Barista Sanusi Umar da Barista Usman Imam da Kwamared Bello Basi suka yi, inda suka garzaya Babbar Kotun Jihar da ke neman ta hana Gwamnatin Jihar, daukar wani kan ginin da harabar kotuna.
Comments 1