Daga: Abbas Yakubu Yaura
Oluwo na Iwoland, Oba Abdulrasheed Adewale Akanbi, a ranar Lahadin da ta gabata ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauki jami’an ‘yan sanda miliyan biyar aiki domin yaki da rashin tsaro a kasar.
Oluwo, a wata sanarwa a ranar Lahadin da ta gabata ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Alli Ibrahim, ya kuma bukaci Buhari da ya mayar da Najeriya kasar ‘yan sanda domin karfafa tsaronta.
KARANTA WANNAN LABARIN: IGP Ya Bada Umarnin Kamo Jaruman Fina-finan Dake Amfani Da Kayan Ƴan Sanda A Shirin Su
Ya kuma shawarci gwamnati da ta samar da na’urar adana bayanai ta zamani da hanyoyin tantance ‘yan Najeriya don baiwa jami’an tsaro damar tambayar duk wani mutum a kasar Najeriya ba tare da wata hanyar tantancewa ba.
Da yake nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a Najeriya, ya bukaci gwamnati da ta aiwatar da tsare-tsaren da za su karfafa tsarin tsaron kasar.
Ya kuma jaddada bukatar daukar karin jami’an tsaro tare da samar da ingantattun kudade.
“A matsayin ka na babban kwamandan sojojin kasa, ya kamata shugaba Buhari ya yi la’akari da daukar ma’aikata kusan miliyan 5 aikin ‘yan sandan Najeriya tare da kara albashin jami’an tsaro a duk wata.
“Najeriya, wacce ba ta kai mutane miliyan 250 ba, tana da karfin ‘yan sanda kasa da 300,000. Baya ga wannan, dole ne gwamnati ta inganta bayanan mu da kuma samar da na’urorin da za su taimaka wa ‘yan sanda samun damar samun bayanan mutum ba tare da la’akari da wurin ba.
“Dole ne a aiwatar da aikin-daukar-katin shaidarku. Da wannan, masu laifi da ‘yan fashi za su yi wahala su zagaya mu,” in ji Sarkin.