By Abbas Yakubu Yaura
Kamfanin jiragen sama na Najeriya mafi girma Air Peace, ya dakatar da ayyukan sa na zuwa filin jirgin sama na Kaduna.
Wata majiya ta bayyana haka ga Jaridar Daily Trust, inda ta alakanta faruwar lamarin ga harin da aka kai a kusa da filin jirgin a karshen mako.
DUBA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Cibiyoyin Kirkire-kirkire Na SDGs Don Bunkasa Tallafin Zaman Takewa Na Jihohi
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito yadda ‘yan bindiga suka bindige wani mai gadi da ke aiki da Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Najeriya (NAMA) a ranar Asabar.
Sojoji sun yi artabu da ‘yan fashin ne lamarin da ya janyo tsaikon jirgin Azman da ke kan hanyarsa ta zuwa Legas.
A ranar Talata ne Azman ya sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragensa na zuwa Kaduna saboda rashin tsaro.
Bayan sa’o’i kadan ne aka samu labarin dakatar da ayyukan kamfanin Air Peace na zuwa Kaduna.
Kakakin rundunar Air Peace Stanley Olisa ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin, amma bai yi cikakken bayani ba.
Comments 1