By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano, Hassan Kauye Farawa, ya kaddamar da rundunar tsaro wanda ta kunshi ‘yan banga da mafarauta 100 domin tallafa wa jami’an tsaro wajen tabbatar da ingantaccen tsarin tsaro a yankin.
Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da jami’an tsaro a wani taron masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro a yankin, shugaban ya bayyana cewa majalisar tana tallafawa jami’an tsaro wajen tabbatar da isasshen tsaro na rayuka da dukiyoyi jama’a.
Na yi bayanin cewa, domin karfafa wa ’yan sandan kwarin guiwa, majalisar ta sanya kowannen su a kan alawus-alawus na kufi Naira 20,000 duk wata daga wannan wata domin karfafa musu gwiwa waje kara himmar su.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa majalisar zata gina ofishin kwamandojin yankin na jami’an tsaro.
Shugaban karamar hukumar ya kuma sanar da bayar da gudunmuwar sabuwar mota ga sashin ‘yan sanda na Ja’oji da kuma bayar da tallafin babura guda 10 ga wasu zababbun mutanen da za su taimaka wa jami’an tsaro wajen tattara bayanan yaki da miyagun ayyuka a karamar hukumar.
Hakazalika, manyan mutane sun halarci wajen bikin ciki harda Hakimin Kumbotso, Alhaji Ahmad Ado Bayero, wanda ya umurci dukkan sarakunan yankin dasu bayar da gudunmawarsu wajen tabbatar da tsaro mai inganci a yankin. .