Rashin Tsaro ya sanya har yanzu ba a bude Makarantu Sakandare 75 a Zamfara – Ma’aikata
Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da cewa ba a bude makarantun sakandire 75 a jihar sakamakon rashin tsaro.
Babban Sakataren Ma’aikatar ilimi, Alhaji Kabiru Attahi ne ya bayyana hakan a yayin wani taro na yini biyu na matakin Jiha don tattauna manufofin kasa kan ilimin jinsi (NPGE) a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: COEASU Ta ce Tana Gab da sake Garƙame Kwalejojin Ilmi, ta tafi Yajin Aiki
Hukumar kula da ilimin bai daya ta Zamfara Universal Basic Education Board (ZUBEB) tare da hadin gwiwar UNICEF ne suka shirya taron.
Ya ce gwamnatin jihar na aiki ba dare ba rana domin sake bude makarantun da abin ya shafa.
Ya kuma jaddada cewa an rufe makarantun ne sakamakon hare-haren ta’addanci da ‘yan bindiga da ke aiki a jihar ke ci gaba da kai wa.
Attahi ya kuma bayyana cewa makarantun da abin ya shafa yawancin su sune sakandiren mata a jihar.
Idan ba a manta ba a watan Satumban 2021 ne gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantu, duba da yadda ayyukan ‘yan bindiga ke karuwa a jihar.
Gwamnan jihar ne ya bada umarnin rufe makarantun firamare da sakandire biyo bayan sace dalibai 75 da aka yi a makarantar sakandiren gwamnati ta Kaya a karamar hukumar Maradun.
Mai ba da shawara kan UNICEF na jihar, Dokta Ahmed Hashim, ya bayyana manufofin kwamitin, wanda ya hada da nazarin abubuwan da aka samu daga taron da ya gabata a kan NPGE, aikin gida ta hanyar tabbatarwa, kammala shirin aiwatarwa da kuma kaddamar da kwamitin aiwatarwa na jihar.