Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyya ga Masarautar Ilorin, gwamnati da al’ummar jihar Kwara kan rasuwar Dakta Abdulkadir Oniyangi.
Shugaban kasa ya mika ta’aziyyarsa ne cikin wata sanarwa da ta fito ta Babban mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai, Garba Shehu a Abuja ranar Asabar.
Cikin sakon ta’aziyyar da Buhari ya mika ga iyalai da abokan arzikin tsohon babban Sakatare da Sakataren Gwamnatin Soja a Kwara a shekarar 1984, Shugaban ya ce za a yi kewarsa saboda gudumawan da ya bayar wajen ci gaban kasa.
Ya ce, mamacin ya yi amfani da kwarewarsa, baiwansa da lokacinsa wajen yi jama’a hidima a matsayinsa na likita da kuma kwararre.
A cewarshi, soyayyar mamacin ga kasa abin yabawa ne, musamman irin yadda yake amsa kiran kowa a duk lokacin da aka kirashi duk wuya, duk runtsi.
Shugaban kasar ya yaba kan rawar da marigayin ya taka wajen zaben shekarar 2015.
Buhari ya jinjina wa marigayin kan sadaukarwar da ya yi a fannin neman ilimi da kuma aiki, musamman samar da Kungiyar daliban Masarautar Ilorin, wanda ta zama mafaka ga duk wadanda suka ci gaba a jihar.
Shugaban kasan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin sannan ya ba iyalansa hakurin jure rashinsa.