Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Sarkin Gujba, Alhaji Tijjani Saleh da kuma gwamnatin jihar Yobe bisa rasuwar mahaifiyar Sarkin, , Hajiya Fanna Ibn Ali Gangarang.
Shugaban kasar ya mika ta’aziyyar ne a wata takarda da Garba Shehu, Kakakin shugaban kasar ya fitar a ranar Asabar a Abuja.
A karshe Shugaba Buhari ya yi addu’a ga mamaciyar tare da nema mata Rahama.