Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa’i ya sanar da rasuwar sarkin Zazzau “Ina mai baƙin cikin sanar da rasuwar uba ga wannan jiha ta mu, mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dakta Shehu Idris CFR. Ya rasu a asibitin rundunar soji dake nan Kaduna bayan gajeriyar rashin lafiya.
Za a yi jana’izarsa a garin Zariya da misalin ƙarfe 5 na yamma da yardar Allah”.
Dukkanin matakan kariyar annobar Korona za a yi amfani dasu a yayin jana’izar tasa.
https://dimokuradiyya.com.ng/da-ɗumi-ɗumi-sarkin-zazzau-alhaji-shehu-idris-ya-rasu/
El-Rufa’i ya ƙara da cewa na sanar da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari rasuwar Sarkin Zazzau ɗin. Shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya Farfesa Ibrahim Gambari zai jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa yin ta’aziyyar Sarkin ga jama’ar Zazzau da ma iyalinsa.
“Mun yi babban rashi, mutum mai nagarta uban dake tafiyar da jihar nan yadda ya kamata. Ina fatan Allah yasa aljanna Firdaus ta zama gida a garesa”, cewar El-Rufa’i.