• Rayuwar harkar fim kamar Makaranta ce inji daya daga cikin jarumai a masana’antan fim na Kannywood wato Sapna Aliyu Maru.
• Ta Kuma ce wasu su yam fim suna son zaman aure Amma wasu na musu bits da kulli wajan kashe musu auren su.
• Sapna Aliyu Maru ta yiwa magoya bayan ta fatan alheri.
Jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood ta bayyana harkar fim da cewa, kamar rayuwar makaranta ce, wadda kowa ya iya allon sa ya wanke.
Jarumar ta bayyana hakan ne ga wakilin jaridar Dimokuradiyya, inda ta ke cewa, “Rayuwar kamar ta Makaranta ta ke, domin kuwa duk yadda ka zo a haka za ka rayu a cikin ta. Idan kana ganin kai kana da rawar kai, sai ka ga akwai wadanda suka fi ka. Idan ilimi ka zo da shi, to akwai wadanda suka fi ka. Komai dai na rayuwa haka ya ke. Don haka yadda ka ita tafiyar da harkar ka da mutane, haka za ka samu kan ka a cikin ta. ”
KARANTA WANNAN LABARIN: Gaskiyar Lamari kan Gwajin Lafiyar Muhuyi Magaji
Mun tambayi Sapna Aliyu Maru ko wanne buri take da shi a cikin masana’antar fina-finai?
Sai ta ce” Buri na dai shi ne na samar da wani abu, da za a rinka tuna wa da ni a nan gaba, don haka ina son na samar da Gidauniya ta taimakon mabukata, domin ya zama ina yin abin da jama’a su ke amfana da shi, kuma ina fatan nan da dan wani lokaci burina, zai kai ga cika”.
Daga karshe ta yi fatan alheri ga masoyan ta da abokan sana’ar ta.
Comments 1