kasar nan a ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai yaki da laifuka da miyagun kwayoyi, Mista Oliver Stolpe, ya bayyana cewa kimanin mutane miliyan 6 a Najeriya su ke rayuwa bisa dogaro da hanyar amfani da miyagun Kwayoyi.
A cewar sa wannan na haifar da babban kalubalen ga kiwon lafiyar jama’ar kasar nan.
Da yake mayar da martani ga rahoton, Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa Mai ritaya ya ce nan ba da dadewa ba hukumar za ta kaddamar da cibiyar kiran waya ta NDLEA wadda kwararru a fannin shawarwari, da tabin hankali, da ilimin sanin halayyar dan Adam, da dai sauransu, za su ba da taimako ga masu shan muggan kwayoyi.
A jiya ne Stolpe ya yi magana a wani taron manema labarai don fara ayyukan bikin ranar Majalisar Dinkin Duniya (MDD) na wannan shekara kan yaki da shan muggan kwayoyi da safarar miyagun kwayoyi mai taken, “Maganin kalubalen Shan miyagun kwayoyi ga lafiyar Bil Adama.”
Ya bukaci gwamnati da ‘yan takarar mukaman siyasa da abokan hulda na kasa da kasa da kada su manta da matsalar rashin lafiyar al’umma da ake fama da ita a kasar nan dangane da Shan miyagun kwayoyi
Shima da yake jawabi a wajen taron, Shugaban kuma Babban Jami’in Hukumar Yaki da Sha da fataucin Muggan Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), Birgediya. Janar Mohamed Buba Marwa Mai ritaya ya ce an kama mutane dubu goma Sha bakwai da dari shida da arbain da bakwai 17,647 masu safarar miyagun kwayoyi da dillalai 10 a cikin watanni 17 da suka gabata.
Ya yin da ya bayyana cewa an yanke wa mutane dubu biyu da dari uku da sittin da Tara 2,369 hukuncin dauri a gidan yari yayin da sama da masu shaye-shayen kwayoyi dubu goma Sha daya ne 11,000 aka basu shawarwari tare da yi musu magani a lokaci guda.
Sai dai Kuma Marwa ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba hukumar za ta kaddamar da cibiyar kiran waya ta NDLEA wadda kwararru a fannin shawarwari, da tabin hankali, da masu ilmin sanin halayyar dan Adam da dai sauransu za su taimaka wa masu shan muggan kwayoyi.
A karshe ya kuma bayyana cewa, cibiyar za ta kuma baiwa masu tsoron kyamar neman taimako ba ta hanyar sirri.