Kungiyar Kwallon kafa ta Real Madrid na tattaunawa da Rennes a yunkurin ta na kammala siyan Dan wasan tsakiyar kungiyar Eduado Camavinga.
Sai dai kafin wannan lokaci kungiyoyin kwallon kafa kaman PGS, Arsenal da kuma Manchester united, sun kasan ce cikin jerin kungiyoyin da suka zuba Ido kan matashin dan wasa.
Matashin Dan wasan mai shekarar 18, kwantaraginsa a kungiyar Rennes dake kasar Faransa, zai kare ne a kakar wasa Mai zuwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Hadaka ta kashe Barayin Mota guda 3 a Imo
Ya yin da a halin yanzu Los Blanco’s take kokarin kammala cinikin shi, a kan kudin yuro Milliyan 30 a yau Talata, da ake kokarin rufe cinikayyar yan wasa.
A cewar wasu ingantattun rahotanni dake fito wa daga Kasar Faransa, na nuna cewa, Madrid ta kammala cinikin Camavinga, inda a yau kungiyar za ta yi Miji gwajin lafiya, kafin ya Sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru 5 a kungiyar.