Zakarun gasar Laliga wato ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta bayyana cewar a wasan farko na Laliga da zata fafata da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Sociedad za tayi amfani da rigarta zaɓi ta uku ne.
Wannan shine karon farko da Real Madrid zata sanya wannan riga, itadai rigar kusan baƙa ce da tsallin pink a jikinta, mahukunta ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Madrid ne suka bayyana hakan ganin cewa ba a taɓa amfani da ita ba.
Idan za a iya tunawa Real Madrid tayi amfani da zaɓin rigarta ta biyu a wasan gasar zakarun nahiyar turai data fafata da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City a wasan zagaye na 16 wato rigar nan mai kalar pink awatan Ogustan daya gabata.
An ƙaddamar da kalar rigar ne wadda akace za a dinga amfani da ita lokaci zuwa lokaci a wannan sabuwar kakar wasan da za’a fara ta 2020 zuwa 2021, Real Madrid dai bata buga wasanta na makon farko ba tsakaninta da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Getafe inda za a iya cewa ya zama kwantai kenan.
A wannan makon zata fafata wasanta inda zata kaiwa Real Sociedad ziyara a wasan mako na biyu kenan na gasar ta Laliga wanda tuni wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan sun lashe wasan farko tun a makon daya gabata.