Biyo bayan gano illar da rigafin COVID-19 na Kamfanin AstraZeneca ke da shi ya tilasta wa wasu manyan kasashen duniya dakatar da rigafin a kasashen su.
Wannan mataki nasu na zuwa ne bayan samun rahotannin yadda jinin wadanda suka karbi rigafin ke daskarewa bayan an yi musu rigafin.
A yanzu haka dai wadannan kasashen sun yi kuruwar cewa ba za su sake ko da wasa a ci gaba da yi wa yan kasashen nasu rigafin na Kamfanin AstraZeneca ba har sai sun gudanar da bincike kan alakar daskarewar jinin da kuma rigafin
Kasashen da suka dakatar da rigafin sun hada da kasar Denmak, Norway, Tsibirin Ailan, Austria da kuma Australia.
Sauran sun hada da Latvia Luxemburg, Lithuania, Ireland, Holand, Bulgaria da Kasar Jamus.
yayin da tuni su ma kasashen Spaniya, Faransa, da iItaliya suka haramta rigafin don kare yan kasashen nasu daga afkawa bala’in da rigafin zai iya haifarwa.