Hukumar dake kula da Magunguna ta Kasar Birtaniya ta ce kawo yanzu ta sake gano mutane sama da talatin da Jinin su ya dasakare bayan karbar Allurar Rigafin Korona na Kamfanin AstraZeneca.
Ko da yake Hukumar ta ce wannan ba yana nuni da cewa hatsarin allurar ya wuce misali ba ne.
Wannan adadin mutane da allurar ta yi musu illa, suna daga cikin mutane sama da miliyan sha takwas ne da aka yi musu rigafin daga 24 ga watan Maris.
Fargabar Daskarewar Jinin ta tilasta manyan kasashe ciki har da Holand da Jamus da Faransa da Canada dakatar da gudanar da rigafin a ƙasashen su.
Sai dai Kamfanin na AstraZeneca ya ce Hukumar Kula da Sarrafa Magunguna ta duniya ta ce Rigafin Kamfanin ba shi da wata da za a yi ta yamaɗiɗi.