Najeriya ta samu tallafin Allurar Rigafin Korona kimanin dubu ɗari daga Kasar Indiya, Kamar yadda ofishin Babbar Hukumar Kasar dake Abuja ya bayyana.
Kamar yadda Kwamishinan hukumar ya shaida, ya ce wannan na zuwa ne a wani Mataki na Firaministan Kasar Indiya Narendra Modi na taimakawa al’ummar duniya fita daga fadawa wannan cuta.
Kazalika kuma hakan na daga cikin yunkurin kara yaukaka dangantaka daje tsakanin kasashen biyu kamar yadda aka sani tun tale-tale.
Kasar Indiya Kaɗai Kawo yanzu ta raba Rigafin Korona sama da Miliyan sittin wa kasashe tamanin da biyu a fadin duniya wanda dukkannin rigafin a kasar aka sarrarfa.