Kasar Norway ta kara kafewa kan bakar ta tare da kara wa’adin hana rigafin Korona a kasar daga yanzu har zuwa ranr 15 ga watan Afirelu don samun damar zurfafa binccike kan allurar rigakafin COVID-19 samfurin AstraZeneca dake ake zargin cewa na daskarar da jinin wadanda aka yi musu.
A makon da ya gabata dai Kungiyar Tarayya Turai ta EU ta karfafa gwiwar jama’a cewa rigakafin ba shi da wata illa kazalika babu gamin shi da daskarar da jinin mutum.
A bangaren ta ita ma Hukumar LAfiya ta Duniya WHO ta bada amannar cewa rigafin lafiya kalau ne don haka kasashe su ci gaba da gudanar da al’amarin gaban su gaba gadi.
“Abu ne mawuyaci mu dauki wannan mataki na kara wa’adin dakatar da rigafin AstraZeneca, to amma hakan shi ya fi dacewa ga kasar mu” Cewaar Daraktan KAre Yaduwar cututtuka na Cibiyar Lafiyar Kasar Norway Geir Bukholm.
Ya kara da cewa “Dole ne mu kara zurfafa bincike kan wannan rigafi indai muna son kan mu da lafiya”.
Wannan Karin wa’adi zai sa ala tilas kasar ta shafe makonni biyu kenan ba tare da an gudanar da rigafin ba, kuma wadanda tun farko aka yi musu sun ci banza kenan ba za a sake musu shi ba.
Idan za a iya tunawa muatne hudu ne suka gamu da ajalin su sakamakon wannan rigafin a manyan kasashen turai.