Is-haq Oloyede’s, wa’adinsa ya Kare a matsayin sa na mai rijistaran hukumar gudanar da jarrabawar samun gurbin shiga Jami’a. Kamar yadda Jaridar the Punch ta wallafa a shafinta
Wa’adinsa yazo karshe tare da sauran hukumomin sha uku dake karkashin Hukumar Ilimi ta gwamnatin tarayya.
Oloyede, an ruwaito cewar ya mika takaddun ofishin ga babban ma’aikacin hukumar ta Ilimi.
KARANTA:- MAI YA YI ZAFI: Harry Kane ya ki zuwa atisaye da tawagar Tottenham
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewar, shugaban Kasa Muhammadu Buhari na iya sabunta wa’adin su, shida sauran shuwagabannin hukumomi sha uku da suka sauka.
Sauran shuwagabannin hukumomi da suka sauka sun hada da Shugaban hukumar jarrabawar NABTEB Farfesa Ifeoma Isiugo-Abanihe, da Sakataren makarantun Jami’a Dakta Hameed Boboyi, da Farfesa Abubakar Rasheed.
Sauran sun hada da Prof. Sunday Ajiboye, Shugaban kungiyar Malamai; Afolabi Aderinto, shugaban hukumar CRCN, Farfesa Garba Dahuwa Azare, shugaban hukumar NTIE; da Farfesa. Michael Afolabi, shugaban hukumar LRCN, Farfesa Steven Ejugwu Onah, shugaban hukumar Lissafi, Farfesa Chinyere Ohiri-Aniche, shugaban hukumar NILN; Farfesa. Lillian Salami, shugaban hukumar NIEPA; Farfesa Lanre Aina, shugaban hukumar NIL; Farfesa Abba Haladu, shugaban hukumar NCML, da kuma Farfesa Bashir Usman, shugaban hukumar NEC.
A wani labarin
An gabatar da masu bautar kasa 1,800 a Jahar Zamfara
Shugaban Alkalai na Jahar Zamfara ya rantsar da sabbin masu bautar kasa dubu daya da dari takwas a garin tsafe dake Jahar Zamfara.
An dayi bukin rantsar da masu bautar kasar ne a wani mazaunin Yan bautar kasan dake kan titin Gusau a garin Tsafe Jahar Zamfara.
Shugaban Alkalan na Jahar Zamfara, Kulu Aliyu, ya yaba da irin ayyukan da matasa masu bautar kasa keyi, inda ya shawarci wadannan sabbin da su zage damtse wajan gudanar da ayyukan tallafawa kasar.
Shugaban kotun Majistret, wadda Lubabatu Aliyu Kanoma, ta wakilta, ya shawarci matasan da su zama masu kyakykyawan dabi’a, su kasance wakilai ne na jahohin su a duk inda suka sami kansu.
Sai dai Kodineta na masu bautar kasar na Jahar Zamfara, Muhammad Namallam Taura, ya taya matasan murna domin samun nasarar kammala karatunsu na jami’a ba tare da matsala ba.
Namalam Taura, ya cigaba da cewa abunda ake nufi da masu bautar kasar, wata dama ce da matasa ke dashi wajan bada gudunmawar su ta yadda za’a ciyar da wannan kasar gaba, musamman ma nan Jahar Zamfara.
Muna fatan zaku bada gudunmawar sosai wajan kawo cigaba a Jahar ta Zamfara.
Ya Kuma janyo hankalin matasan dasu kasance sun bada gudunmawar su, suna shiga duk wani aiki da ya shafe su.
Namallam Taura, ya yabawa shuwagabanni da jagororin matasan baki daya na jahar Zamfara.
Ya kuma shawarce su da su cigaba da tallafawa kada su gaji har karshe.
a yayin gudanar da rantsuwar dai an lafta wani mamakon ruwan sama.