By Ishaq Dabai
Biyo bayan hare haren na baya bayan nan da aka kai kan wasu membobin jam’iyyun siyasa yayin tarukan su a Nnewi da Nnobi da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka yi sanadiyyar rasa rayukan mutane hudu tare da kona wasu motoci, Kwamishinan‘ yan sandan jihar Anambra, Mista Tony Olofu ya umarci jam’iyyun siyasa dake shiga cikin zaben gwamna mai zuwa a jihar don mika jadawalin tarukan su ga hukumar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar DSP Toochukwu Ikenga yace jadawalin zai taimaka wa ‘yan sanda wajen tabbatar da tsaro a duk wuraren da ake gudanar da harkokin siyasa.
Yace“Kwamishinan yayi nuni da cewa yakin neman zabe wani muhimmin bangare ne na tsarin zaben.
Wannan don haka, zai ba rundunar ‘yan sanda damin samar da isasshen tsaro don kare lafiyar mahalarta a irin wannan taron, haka kuma zai taimakawa rundunar ta tura sauran rukunoni na dabaru da na aiki, da kuma ‘yan sanda masu kula da zirga zirgar ababen hawa zuwa mahimman wuraren don tabbatar da cewa jama’a sun ci gaba da samun tsaro a jihar. ”Ana sa ran kungiyoyin zasu gudanar da sintiri na tsaro, sa ido, kula da zirga zirgar ababen hawa da sintiri tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro ‘yan uwan juna.
“Tabbas wannan zai hana ‘yan daba su kaddamar da hare hare a kan amintattun jam’iyya da kuma tabbatar da tsaro irin wannan.” CP, duk da haka, yana gargadin irin wadannan jami’an da za a tura don wannan aikin dasu nuna kwarewar aiki cikin yanayin bin doka.