By Abbas Yakubu Yaura
Wasu daliban makarantar Sakandare dake garin Abeokuta na jihar Ogun, sun jefi jami’in ‘dan sanda (DPO) na sashen Obantoko, Alimeke Ignatius da duwatsu, inda suka raunata kansa, a wani rikici daya barke tsakanin daliban wasu makarantu biyu a cikin babban birnin.
Wakilinmu ya tattaro cewa daliban makarantar Egba Comprehensive High School da Asero High School dake garin Asero, a Abeokuta, sun yi arangama da junan su.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa daliban da suka jefi juna da duwatsu da wasu abubuwa sun tare babbar hanyar, lamarin daya haifar da tashin hankali a tsakanin mazauna yankin.sai dai kuma domin kwantar da hankulan masu fadan, an kira jami’an ‘yan sanda na ofishin ‘yan sanda na Obantoko dasu kawo karshen lamarin.
Jaridar Aminiya ta gano cewa DPO din ya jagoranci tawagar mutanensa zuwa wurin da lamarin ya faru sai dai daliban da suke tashin hankalin sai suka far musu.
Rahotanni sun ce daliban sun yi jifa da duwatsu kan jami’an inda suka yiwa Ignatius rauni a kai.
DPO ya samu munanan raunuka a kansa yayin da aka garzaya da shi wani asibiti da ba a bayyana ba domin kula da lafiyarsa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar wa da wakilinmu faruwar lamarin, inda yace lamarin ya faru ne a ranar Litinin.
Oyeyemi ya ce daliban makarantar Egba Comprehensive High School da na Asero sun yi artabu da jami’an ‘yan sanda daga ofishin Obantoko domin su dauki nauyin lamarin.
“An jefi DPO da duwatsu. Daliban sun yi ta jifan juna da duwatsu da sauran abubuwa a yayin fadan,” inji shi.
Da aka tambaye shi ko an kama su, Oyeyemi ya ce, “Ba za mu iya kame daliban ba saboda kananan yara ne. Mu kawai za mu iya tsare su da yi musu nasiha, bayan haka za a sake su.
Shugaban PCRC na jihar Samson Kunle Popoola, a wata sanarwa dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Babatunde Odeyemi, ya koka da yadda daliban makarantun sakandire ke haddasawa jama’a a jihar, yana mai cewa, “Idan ba a gaggauta tantance hakan ba, hakan na iya nuna babban abin mamakin hadari ga makomar kasar nan.”
Kazalika Idan dai za a iya tunawa dai a kwanakin baya ne daliban makarantar Sakandare a jihar Ogun suka fara kai farmaki kan malamansu a duk lokacin da aka hukunta su kan duk wani hali na rashin da’a da suka aikata.