Kamfanin dillancin labaran reuters ya ruwaito majiyar ma’aikatar tsaron kasar ta Taiwan cewa, kasar Sin ta harba wasu makamai masu linzami na Dongfeng da dama a cikin ruwa a kusa da gabar tekun Taiwan na arewa maso gabas da kudu maso yammacin kasar, tun daga karfe 13:56 agogon kasar Sin, dai dai da karfe (06:56 agogon GMT).
Makamai masu linzami na Dongfeng na sojojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin ne ke sarrafa su.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya ruwaito cewa, ma’aikatar tsaron Taiwan ta ce ta kunna wani tsarin tsaron da ke kareta, a matsayin martani ga harba makamin, inda ta kara da cewa ta yi Allah wadai da matakin rashin hankali na kasar Sin, wanda ya zai lalata zaman lafiya a yankin.
Zaben 2023: Kar Ku Amince Da Yin Magudi — Fasto Enenche Ya Gargadi Jami’an INEC
A wnai labari kuma na daban.
Zaben 2023: Kar Ku Amince Da Yin Magudi — Fasto Enenche Ya Gargadi Jami’an INEC
Yayin da zaben 2023 ke gabatowa, Babban Fasto na Cibiyar Bishara ta Duniya ta Dunamis, Paul Enenche ya yi gargadi game da magudi a zaben dake ta fe
Enenche ya bayyana cewa magudin zabe ba zai yi aiki ba a halin da Najeriya ke ciki.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake hudubarsa a hedikwatar cocin, Glory Dome da ke Abuja a daren jiya Laraba.
Limamin ya kuma bukaci jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da su bijirewa yunkurin magudin sakamakon zabe mai zuwa.
A cewar Enenche: “Babu wani tsari na shaidan da magudi da zai yi aiki a wannan lokaci da muke ciki.
“Babu tsarin cin hanci da rashawa da zai yi aiki. Muna matsawa zuwa wancan gefen kuma babu abin da zai iya hana shi.
“Ya kamata mutane su dage su yi abin da ya dace, idan kana aiki a INEC ka yi abin da ya dace.
“Idan kafofin watsa labarun sashenku ne, kada ku ƙyale mutane su ba ku kuɗi don tura bayanan da ba da ce ba.