Ana ci gaba da samun takaddama Kan Shirin Gudanar da Zaben fidda Dan takarar Gwamnan a Jihar Osun, dai dai lokacin da Jam’iyyar APC Ta shirya Gudanar da shi a yau.
Akwai dai Mutane guda biyu da kowannensu yake ganin cewa ya cancanta, domin samun tikitin tsayawa takarar Gwamnan Jihar.
Daga cikin mutanen da suke wannan takaddama a Jam’iyyar APC Ta Jihar Osun, sun Hadar da Gwamnan Jihar Gboyega Oyetola da kuma tsohon sakataren Gwamnatin Jihar Moshood Adeoti.
Adeoti dai ya kasance tsohon Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar, kuma Yana da goyon bayan ministan cikin gida na tarayya Obgeni Rauf Aregbesola.
To Sai shima daya Dan takarar Wato Oyetola ya kasance sunyi aiki tare da Ministan tsawon Shekaru 8, lokacin da yake Kan kujerar Gwamnan Jihar.
Wannan alaka da suke da ita da Ministan Mai ci, ta Sanya ake ta tababa Kan Wanda zai iya darewa wajen nasara a wannan Zaben fidda gwani.