By Abbas Yakubu Yaura
Mutum daya ya mutu a daren Juma’a a wata arangama tsakanin matasa ‘yan kabilar Anguwan Taya da Yalwan Tsakani wanda ya kai wasu sassan unguwar Yelwa da ke cikin birnin Bauchi tare da jikkata wasu mutum hudu.
Ko da yake ba a san musabbabin faruwar rikicin tsakanin matasan yankin ba, an tattaro cewa rikicin ya samo asali ne sakamakon fifiko a tsakanin matasan.
Gwamnatin Ekiti Ta Haramta Amfani Da Rawani Da Sandan Girma Ga Sarakunan Gargajiya Wadanda Ba Oba Ba
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi (PPRO), Ahmed Mohammed Wakil, ya sanar da hakan a wata sanarwar manema labarai da ya sanyawa hannu, kuma ya baiwa Jaridar DAILY POST a ranar Asabar da ta gabata cewa, an sanar da ‘yan sandan rikicin da misalin karfe 10 na daren ranar Juma’a.
Ya ce binciken farko da ‘yan sandan suka gudanar ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne sakamakon adawa tsakanin matasan.
“A ranar 27/05/2022 da misalin karfe 10:00 na rana, an yi wata arangama a Yelwan Tsakani, Lushi da Uguwan Kusu.
“Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne biyo bayan wata hamayya tsakanin matasan Anguwan Taya, da Yalwan Tsakani wanda ya kai wasu sassan Yelwa.
“Sakamakon haka, an kona gidaje biyar, mutane hudu sun samu raunuka daban-daban, daya kuma likita ne ya tabbatar da mutuwarsa,” in ji SP Wakil.
Kakakin ‘yan sandan ya sanar da cewa, ‘yan sandan na kan gaba a lamarin domin an tura jami’ai zuwa yankin da abin ya shafa da nufin wanzar da zaman lafiya da kuma hana ci gaba da tabarbarewar doka da oda.
“A halin da ake ciki, jami’an ‘yan sanda da suka hada da ‘yan sandan fasaha, dana wayar tafi da gidan ka da RRS da kuma QIU sun yi gaggawar mayar da martani ga halin da ake ciki.
Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Umar Mamman Sanda ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin tare da yin kira da jama’ar birnin su kwantar da hankula.
A cewar PPRO, “Kwamishanan ‘yan sanda CP Umar Mamman Sanda ya bayar da umarnin a gudanar da bincike na gaskiya don gano al’amuran da suka faru tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika aika a gaban kuliya.
“CP ya kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankulan su kuma su ci gaba da gudanar da harkokinsu na halal kamar yadda aka dawo da zaman lafiya a yankin da abin ya shafa, don Allah.”
Comments 1