By Abbas Yakubu Yaura
Lauyan dake kare hakkin dan Adam, Mista Femi Falana (SAN), ya yi kira ga jami’an ‘yan sanda da su kamo matar tsohon Gwamna Willie Obiano, Ebelechukwu; da kuma tsohuwar jakada a Spain, Bianca Ojukwu, wacce kuma matar shugaban Biafra ce, Chukwuemeka Ojukwu.
DUBA WANNAN LABARIN: Yajin Aikin ASUU: BUK Ta Umurci Dukkan Dalibai Da Su Bar Harabar Jami’ar
Falana ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya aikewa jaridar PUNCH a ranar Juma’a yayin da yake mayar da martani kan fadan da mata biyu suka yi a bikin rantsar da gwamnan jihar Anambra Farfesa Charles Soludo a ranar Alhamis.
Babban Lauyan ya ce ‘yan sandan su yi gaggawar cafke su biyu idan ba manyan mutane ba ne.
Ya kara da cewa, “Ba shakka Gwamna Soludo ya ba da hakuri kan abin kunyar da aka a wurin bakin. To amma lamarin bai kawo karshen wannan laifin ba. Laifin fushi yana faruwa ne lokacin da mutane biyu ko fiye suka yi faɗa a cikin jama’a.
Sannan ya kara da cewa ana hukunta duk wanda ya aikata lafi irin wannan a ƙarƙashin sashe na 83 na kundin laifuffuka.
“Kasancewar ba a kama manyan jami’an VIP guda biyu ba ya sake tabbatar da cewa Najeriya na aiki da dokoki guda biyu, daya na masu hannu da shuni daya kuma ta talakawa.
Kazalika yace idan da ma’aikata biyu sun yi ta’adi a wannan bikin, da an kama su, an tsare su, a kuma tuhume su da laifin kawo cikas a bikin rantsar da sabon gwamnan.”