Hukumar ‘yan sanda sun kama Favour Tochukwu ‘yar Shekaru 34 a duniya bisa laifin cakawa makociyarta Joy Asoya ‘ya shekaru 32 a duniya wuka biyo bayan wani rikici da ya barke a tsakaninsu.
Lamarin ya faru ne a unguwar Alhaji Alimi kuma jami’an ‘yan sanda sun kama ta tare da kulle ta a caji-ofis din dake Bariga a jihar Legas.
Wadda aka dabawa wukar an yu gaggawar kaita asibiti ciki har da maigidanta domin ganin an ceto rayuwarta.
Bayan da aka samu wukar da ta aikata laifin, Tochukwu ta amsa laifin da ake zarginta da shi.
DSP Elkana Bala, wanda shi ne kakakin hukumar ya shaidawa manema labarai cewa “yanzu ana gudanar da bincike, daga karshe zamu tura ta kotu domin kammala bincike”.